MAFI SOYUWAR MUTANE AWAJAN ALLAH DA MAFI SOYUWAR AIKI A WAJAN ALLAH




Daga Ibn Umar رضي الله عنهما yana cewa,wani mutum yazo wajan Annabi ﷺ,sai Yace;-
"Ya Manzon Allah;-

*Acikin mutane wanene mafi soyuwa a wajan Allah??*.
Kuma acikin aiyuka;-
*Wani aikine yafi soyuwar aikin awajan Allah??*

Sai Manzon Allah ﷺ yace;-
*(Mafi soyuwar mutane a wajan Allah,shine wanda yafi amfanar da mutane,ko wanda mutane sukafi amfanu da shi,kuma mafi soyuwar aiki a wajan Allah*

*-Farin ciki da zaka sanya azuciyar musulmi*

*-Ko kuma ka yaye masa bakin ciki ko wata damuwa*

*-Ko ka biya masa bashi*

*-Ko magance masa yinwa dake damunsa*

*Wallahi nayi tafiya tare da dan uwana cikin baya masa buqatarsa,shi yafi soyuwa a gareni fiye da nayi i'itikafi a Masallaci na tsawon wata guda,kuma dukkan wanda ya kame daga fishinsa,to Allah zai rufa masa al'aurarsa "wato zai rufa masa asirinsa"*

*Duk wanda ya hadiye fishinsa kuma ina da ikon daukar mataki,Allah zai cika masa zuciyarsa farin ciki a ranar alqiyama*

*Dukkan wanda yayi tafiya cikin buqatar dan uwansa har buqatarsa ta biya,to Allah zai tabbatar da dugadiginsa a ranar da dugadigi suke zamewa*

*Kuma lallai munanan halaye suka bata aiyuka,kamar yanda Khallu yake bata zuma)*
@صححه الألباني في
السلسلة الصحيحة - رقم : (906)

ابن رجب الحنبلي رحمه الله:
Yana cewa;-
"A jumlace wannan Hadisin yana tabbar mana mafi alkhairi aciki mutane,shine wanda yafi amfanar mutane,da wanda yafi hakuri acikin cutarwar da mutane sukeyi masa,kamar yanda Allah ya siffanta bayinsa masu Taqwa da fadarsa":-
*﴿الَّذِينَ يُنْفِقُونَ فِي السَّرَّاءِ وَالضَّرَّاءِ وَالْكَاظِمِينَ الْغَيْظَ وَالْعَافِينَ عَنِ النَّاسِ وَاللَّهُ يُحِبُّ الْمُحْسِنِينَ﴾*
@لطائف المعارف:(٢٣١)

الحسن البصري رحمه الله:
Yana cewa;-
"Wallahi na biyawa musulmi wata buqatarsa shi yafi soyuwa a gareni fiye da nayi sallah raka'a dubu ta nafila".
@قضاء الحوائج:(٤٨)


Allah ne mafi sani.


hakika akwai samun matsayi da lada mai tarin yawa cikin taimakon dan uwanka musulmi cikin biya masa buqatarsa da kuma amfanar da mutane da janyo masu wani abu mai amfanar da su.

Manzon Allah ﷺ yafi kowa janyoma al'umma amfani da alkhairi sannan Sahabban yardaddun Allah.


Allah ya bamu ikon koyi da su baki daya.

Previous
Next Post »

Welcome to ATIOSA Official Website. Atiku Auwal Old Students Association.