Yadda Ake Yin Sallar Jana'iza



'YAN-UWA mafi yawancinmu, muna yin Sallar Jana'iza amma kuma ba mu san abinda ake fada a cikin kowacce Kabbara ba. Dan haka ya sa muka ga cewa yana da kyau mu ware mana wani lokaci na musamman, Domin fahimtar
da mu yadda ake yin sallar Jana'za.


'YAN-UWA ita dai Sallar janai'za, tana da babban lada, ga wanda ya aikata
ta kamar yadda Manzon Allah (SAW) ya koyar, dan haka yana da kyau, mu tsaya mu koya.


Kamar yadda na ce, sallar jana'za tana da kabbarori guda hudu ne
kawai kuma kowacce Kabbara da abin da ake fada a cikinta.

1. KABBARA TA FARKO ana karanta {suraul-fatiha} ne kawai, banda wata sura, ko wata a'ya.

2. KABBARA TA BIYU ana karanta Salatin Annabi ba wani salati na daban ba.

3. KABBARA TA UKU ana yin addu'a ga wanda ya mutu mace ko namiji.

4. KABBARA TA HUDU za ka yi addu'a ne a kanka da sauran al'ummar Musulmi.


DAN UWA KANA GAMAWA sai ka jira Liman ya yi sallama. Ita kuma sallamar guda daya ce tak! Kuma za ka yi ta ne a bangaren damanka.


Allah muke roko da ya kara tabbatar damu akan Sunnar Annabin Rahama, Manzon Allah (S.A.W).


Akwai bukatar a yada domin 'yan uwa musulmai su karu.
ABOKI NAGARI !!


Annabi SAW yana cewa:- "Mutum yana tafiya ne akan dabi'ar Abokin sa. Don haka kowa a cikinku ya duba yaga da wa ya kamata yayi abota".

Sayyadina Umar Allah ya kara masa yarda yanacewa: "Babu wata ni'ima bayan ni'imar musulunci data wuce abaka aboki nagari. Don haka duk wanda ya dace da aboki nagari a cikin ku yayi riko dashi Qaaam".


Imamul-shafi'I Allah ya jikan sa da rahama yana cewa:-
"In Allah ya azurta ka da aboki nagari to ka rike shi Gam da hannunka, Domin samun Aboki nagari abune me wahalar gaske, kuma rasashi abu ne mai saukin gaske".


Imam Hasanul Basari yana cewa:-
"Muna son Abokan mu nagari fiye da yanda muke son Iyalanmu da 'ya'yan mu. Domin
iyalan mu da 'ya'yan mu suna tuna mana Duniya.


Shi kuma Aboki Nagari yana tuna mana Lahira ne, Yace yana daga Siffar Aboki nagari ya fifita
bukatarka akan tasa bukatar".


Luqmanul Hakim yake
cewa da 'Dansa.Ya kai 'Dana, farkon Abunda zaka tsururuta arayuwar ka bayan imani da Allah shi ne Aboki nagari. Domin Aboki na gari tamkar bishiya ce, in ka zauna akasanta, sai  inuwarta ta lullubeka gabarin Rana. In ka tsinki Dan itacenta ta kosar dakai daga yunwa. In har bata anfanar da kai ba kuma bazata taba cutar da kai ba. Allah ka bani Aboki nagari, kasa in zama nagari da kuma sauran al'ummar musulmai bakidaya.


Duk aboki nagari zai so wannan sako zuwa
ga abokinsa, don ya samu falalar abin da zai zama alkhairi agareshi. da sauran Musulmi...


GODIYA GA ABOKAINA NAGARI!!!

Previous
Next Post »

Welcome to ATIOSA Official Website. Atiku Auwal Old Students Association.