ƙungiyar Tsofaffin Ɗaliban Makarantar Atiku Awwal na Gayyatar Ku Zuwa ga Bikin Yaye Ɗaliban Makarantar Karo na 13

Atiosa

Assalamu Alaikum Warahmatullah. Bayan gaisuwa irin ta addinin musulunci. Wannan Ƙungiya na Tsofaffin ɗaliban Makarantan Atiku Awwal Madarasatul Islamiyyah wato ATIOSA

Tana farin cikin gayyatar kowa da kowa zuwaga Bikin yaye Ɗaliban wannan Makaranta karo na goma sha Uku 13, Idan Allah yaso ya yadda. 



Wannan Biki ze gudanane kamar haka.
Ranar Asabar da lahadi, 19 da kuma 20 ga watan febreru, Shekara ta dubu biyu da Ishirin da biyu Miladiyya, Insha Allah. Wanda Saukan Maza ze kama ne ranan Asabar karfe 9:00am Zuwa 1:00pm Insha Allah. Na mata kuma Ranar Lahadi daga karfe 9:00am zuwa 1:00pm Insha Allah. A adereshi kamar haka, No1 Lome Cresent Unguwan Rimi Kaduna.

A wannan Biki da za'a gudanar me Albarka, ranan yaye ɗalibai Maza, to mazane kawai zasu halatta, haka zalika ranan yaye ɗalibai mata, Mata ne kawai zasu halatta. Ba'a yadda wani jinsi ya hallata ba aranar da ba jinsin su ake yayewa ba. Sede idan ya kasance yana daga cikin Wakilai ma'ana (Officials), kokuma wani uziri me karfi.

Wannan Bikin sauka ze gudana ne badan komai ba, sedan ataya su wadannan Ɗalibai da Allah ya baiwa ikon kammala wani sashi na neman Ilimi a cikin rayuwarsu. Akarshe muna rokon Allah ya dataddamu gabaki ɗaya. Kuma yabamu ikon anfani da abunda muka sani na ilimi. Allah ya bamu ikon halatta baki ɗaya. 

Daga Karshe Wannan Ƙungiya me Tarin Albarka tana gayyatar Ƴan Uwa da Abokan Arziki zuwa Walimar da ta tanada domun Karrama waɗannan Ɗalibai. Wanda ze gudana a ranar litini 21 ga watan febreru, 2022. Insha Allah. Allah yabada ikon halatta. Ameen

Wassalamu Alaikum

Previous
Next Post »

Welcome to ATIOSA Official Website. Atiku Auwal Old Students Association.