TSOFAFFIN DALIBAN MAKARANTAR ATIKU AUWAL ISLLAMIYYA
ATIOSA KARKASHIN JAGORANCIN SHUGABAN KUNGIYAR MAL Uthman Muhammad, TA GUDANARA DA YANDA AKE SHIRYA
MAMACI TUNDA DAGA WANKAN GAWA SANYA, LIKAFANI, SALLAH HAR IZUWA MAKABARATA KAMAR YANDA ADDININ MUSULUNCI YA SHIRYA.
YADDA AKE YIN SALLAR GAWA
Dukkanin Malamai na Mazhabobi sunyi ittifaqi akan cewa SALLAR GAWA (JANAZAH) FARILLAH CE TA KIFAYAH.
(wato irin farillar nan
wacce wani zai iya dauke wa wani).
Sai dai an ruwaito daga Asbag (daya daga almajiran Imamu Malik)
cewar Shi Sunnah ce awajensa.
Za'a iya yin Sallar gawa akowanne Lokaci ko dare ko rana, Inji IMAM
SHAFI'IY (RAH).
Amma IMAMU AHMAD DA IMAM ABU HANEEFAH (RAH) Sunce Makruhi ne ayi sallar Janazah alokutan nan guda Uku.
1. bayan Sallar asubah har zuwa fitowar rana.
2. Bayan sallar la'asar har zuwa faduwar rana..
3. Lokacin da Limamin Jumu'a ya hau kan mimbari yake khudubah.
Shi kuwa IMAMU MALIK (RAH) Yace za'a iya yin Sallar Janazah
akowanne lokaci in banda lokacin fitowar rana da kuma lokacin
faduwarta, yace Makruhi ne.
SHARUDANTA:
Dukkan Maluman Mazhabobin sunyi ittifaqi akan cewa wadannan sune
sharudan ingancin Sallar Janazah:
* Tsarki da alwala.
* Suturce Al'aurah.
* Kallon Alqiblah.
Amma Sha'aby da Ibnu Jareer sunce za'a iya yi ko ba tare da alwala
ba.
Imam Shafi'iy da Abu Yusuf sunce Limami yana tsayawa ne adaidai kan
mutum Namiji, ita kuma mace Liman zai tsaya ne adaidai tsakiyar ta.
Amma IMAMU MALIK DA IMAM ABU HANEEFAH Sunce Liman zai
tsaya ne adaidai Qirjin Namiji, ita kuma mace zai tsaya ne adaidai
adaidai tsakiyarta.
KABBARORINTA :
Kabbarori hudu ake yi asallar janazah abisa ittifakin Mazhabobin nan
hudu.
Sai dai an ruwaito Kabbara 3 daga Imam Ibnu Sireen.
Sannan akwai wata ruwayar daga Abdullahi bn Mas'ud (rta) yace:
"Manzon Allah (saww) yayi kabbara 9 abisa Janazah, Sannan yayi 7,
Sannan yay 5, Sannan yayi 4. Kuyi ta kabbarawa mutukar Limaminku
ya kabbara. Koda ya Qara abisa hudu to sallar ba ta 'baci ba".
Imamush-Shafi'iy yace Zaka cira hannuwanka zuwa kafadunka ayayin
dukkan kabbarorin. Amma IMAMU MALIK DA IMAM ABU HANIFAH
sunce ba zaka cira hannuwanka ba sai dai akabbarar farko kawai..
Karanta Fatiha bayan kabbarar farko, Farilla ne awajen Imam Shafi'iy
da Imamu Ahmad. Amma Imamu Malik da Abu Haneefa Sunce BA ZAKA KARANTA KOMAI BA DAGA CIKIN AYOYIN ALQUR'ANI.
Sannan ana yin Salatun Nabiyyi (saww) sannan kuma sai Addu'a ga
mamacin da sauran al'ummar musulmi abayan Kabbara ta biyu data uku
da ta hudu respectively.
Sannan mutum zai yi sallama ne guda biyu abisa Mazhabobi uku.
Amma Hanbaliyya sunce Sallama daya zaka yi a damanka.
Aduba Thamrud-dany Babin Sallar Janazah da kuma Rahmatul-Ummah
shafi na 81.
KUNGIYAR Atiosa TA SHIRYA HAKANNE MUSAMMAN GA
DALIBAN MAKARANTAR
BISA LURA DA LA'AKARI DA YANDA ILIMIN ABIN YAYI KARANCI ACIKIN AL'UMMAH.
MUNA ROKON ALLAH YA SANYA MANA A MIZANIN AYYUKANMU NA LADA UBANGIJI YA JIKAN WAINDA SUKA RIGAMU GIDAN
GASKIYA.
Ga Wasu daga cikin hotunan yanda abun ya kasance tun daga Sallah har izuwa makabarta.
Ga Malamar mu, Malama Suwaiba Abubakar. Allah ya kara mata Albarka. Wacce ta jagoranci gudanar da wannan aikin alkhairi a ilimance.
Ya Allah ka sakama Malaman mu da Aljannah. Ameen.
ConversionConversion EmoticonEmoticon