Alwala da Sallah |
YAU LARABA 12/09/1443 DAI-DAI DA 13/04/2022 KUNGIYAR
TSOFAFFIN DALIBAN MAKARANTAR ATIKU AUWAL ISLLAMIYYA ATIOSA. KARKASHIN JAGORANCIN HAZIKIN JAGORA SHUGABAN KUNGIYAR MAL, Uthman Muhammad.
TA GABATAR DA YANDAAKEYIN ALWALA DA KUMA YANDA AKEYIN SALLAH KAMAR YANDA ANNABI YA KOYAR
DAGA CIKIN MALAMAN DA SUKA KARANTAR DA DALIBAN
- Ustaz Ibrahim Said
- Comd Mubarak Umar
USTAZ USMAN_MUHAMMAD_KABIR YA KARANTAR DA YANDA AKEYIN ALWALA
COMR Saeed Suleiman YA KARANTAR DA YANDA AKEYIN SALLAH
YADDA AKE YIN ALWALA A AIKACE
SALLAH bata yiwuwa saida alwala kuma tilas alwalar ta zamanto anyi
ta da ruwa mai tsarki wanda shine: ruwanda bai canja daga asalin
kamanninsa na ruwa ba,kamar ruwan kogi ko na rijiya ko na idaniyar
ruwa ko na korama.
A KULA DA KYAU:Komai kankantar najasa takan lalata ruwan da yake
dan kadan,amma idan yana da yawa to najasa bata lalata shi har sai
idan ta canja masa kala ko dandano ko kuma kamshi.
1. Ana fara alwala da sunan Allah (Bisimillah) kuma an so a fara da
wanke tafukan hannu a kuma tabbatar sun fita,za ayi hakan sau
uku,musamman ga wanda ya farka daga barci.
A ƘULA DA KYAU:Ba a son a wanke wata gaba sama da sau uku
wannan makaruhi ne.
2. Sannan sai kuskurar baki,tilas ne ayi kuskura na farko,amma idan
aka yi sau uku to shi yafi soyuwa kuma yafi falala.
A KULA DA KYAU: Zuba ruwa a baki kadai baya wadatarwa,dolene sai
an kurkura shi acikin bakin.kuma anso mutum yayi asuwaki yayin
kuskure bakin.
3. Sannan sai shaka ruwa a hanci,tilas ne ayi sau daya a kalla,amma
idan anyi sau uku shi yafi falala.
A KULA DA KYAU: Itama shakar hanci ba wai kawai za'a shigar da
ruwa hanci bane,dole ne ya zamo ta hanyar shakar ruwa tare da
numfashi,kuma ya shigar har cikin hancin sannan ya fyato shi ya fito
tare da numfashi.
4. Sannan sai wanke fuska,itama tilas ne ayi sau daya a kalla,amma
idan anyi sau 3 shi yafi.Za a wanke ta ne tun daga kunnen dama zuwa
na hagu,wannan a kwance kenan,a tsaye kuma tun daga karshen haba
har yazuwa mabubbugar gashin kai.
A KULA DA KYAU: Idan gemun mutum yana da yawa to an so ya
tsefe shi,amma idan bashi da yawa to tilas ne ya tsefe shi ta yadda
ruwa zai ratsa shi.
5. Sannan sai wanke hannaye tun daga 'yan yatsu har zuwa guiwar
hannu,tilas ayi na farko amma idan an kara zuwa sau uku wannan shi
yafi.
A KULA DA KYAU:Ana so a fara da hannun dama kafin na hagu,da
kuma cuccudasu.
6. Sannan sai shafar kai baki dayansa,mutum zai shigar da yan
yatsunsa guda biyu manuniya (sabbaba) cikin kofofin kunnuwansa,sannan
ya shafi fatun kunnuwansa da manyan yan yatsun nasa (ibham)
A KULA DA KYAU:Inda ya wajaba a shafa akai shine:daga mafarin
fuska zuwa kewa,da juyo dashi daga keya zuwa mafarin fuska.kuma
idan gashi yana da yawa ba lallene sai an shafi wanda ya sauko ba.Idan
kuma babu gashin kwata-kwata to sai a shafi fatar kai kuma tilas ne a
shafi fatun kunnuwa.
7. Sannan sai mutum ya wanke kafafuwansa shima sau daya ne ya
wajaba,amma idan akayi sau uku yafi falala.
FA'DAKARWA
1, wuraren da ake yankewa a yayin alwala guda hudu ne.
(a) kurkurar baki da shaka ruwa da wanke fuska.
(b) hannaye
(c) shafar kai da kunnuwa
(d) kafafuwa zuwa idan sawu
2 Tilas ne a wanke wadann gabbai a jere daya-bayan daya,idan kuwa
aka bar wata gabar ba a wanketa ba har jiki ya bushe,to alwala ta
baci,sai a fari wata.
3. An so mutum idan ya kammala alwalarsa yace: "ASH-HADU
ANLAILA'HA ILLALLAHU WA ANNA MUHAMMADAN ABDUHU WA
RASULUHU"
MA'ANA "Na shaida babu abin bauta bisa cancanta sai Allah shi kadai
yake bashi da abokin tarayya,kuma na shaida Annabi Muhammad bawan
Allah ne kuma Manzonsa ne.
KUNGIYAR Atiosa Atiosa TANA SHIRYA WAINNAN ABUBUWAN NE DOMIN ZABURAR DA DALIBANMU.
MUNA ROKON ALLAH YA SANYA MANA ALBARKA MARA IYAKA.
YA KARA TAIMAKONMU CIKIN ABUBUWAN DA MUKA SANYA A GABA.
YA BAMU IKON CIGABA DA GUDANARWA.
ConversionConversion EmoticonEmoticon