Ziyarar Bazata da Wani Tsohon Malamin Makarantar Atiku Auwal Yakawo ma Ƙungiƴar Atiosa da kuma Makarantar Gaba Ɗaya Malam Hudu Hussaini


A yau ne Allah Ya Albarkaci wannan ƙungiya mai albarka da tarban babban malami kuma tsohon malami a wannan makaranta mai Albarka, Malam Hudu Hussaini.

Malam Hudu ya kasance Mutum me nagarta da kuma san taimakon bayin Allah, musamman wurin abunda ya shafi cigaban rayuwa da kuma habaka Addinin Musulunci. Kuma mahaddacin Alqur'ani mai girma, Sa'annan Ɗan uwa ne ga Malam Sani Hussaini, Malami ne a makarantan Atuku Awwal.




Bayan kammala baiwa ɗalibai masu hazaka ƙysututtuka ne muka sama isowar wannan Malami mai tarin Albarka. A inda kowa yayi farin ciki da zuwar sa. Saboda yazo a dede lokacin da ya dace. Bi ma'ana yazo a sanda wakilan wannan ƙungiya ta Atiosa sunanan a wannan makaranta a wannan halin da ake ciki.

Wannan ƙungiya tayi matuƙar farin ciki da zuwan Malam Hudu hussaini wannan makaranta a wannan rana. Kuma ta karrama shi yanda ya kamata.

Bayannan ƙungiyar Atiosa ta nemi Malam Hudu Hussaini da ya bada aran lokacin sa koda babu yawa wajan bayar da shawarwari ga dalibai masu neman illimi.



Kuma yayi maganganu dayawa masu matuƙar mahimmancin da bazasu misaltu ba. Allah muke roƙo da ya karama Malam Albarka a cikin rayuwar sa. Kuma ya kareshi daga kowani irin Sharri. Yasa Aljannah tazamto makoma a gareshi, Ameen

Previous
Next Post »

Welcome to ATIOSA Official Website. Atiku Auwal Old Students Association.